Abacha: Za a maido wa Nigeria dala miliyan 300

0
1174

Daga Usman Nasidi

Gwamnatin kasar Najeriya ta ce tana tattaunawa da kasar Switzerland a kan maido da dala miliyan dari uku da suka ce tsohon shugaban sojin kasar Sani Abacha ya sace.

Ministan harkokin wajen Najeriya, Geoffrey Onyeama,ya ce tuni aka kwato dala miliyan dari bakwai daga Switzerland din.

Kungiyar da ke yaki da cin hanci ta kasa da kasa, wato Transparency International ta zargi marigayi Sani Abacha da sace kimanin dala biliyan 5 a lokacin mulkinsa daga shekarar 1993 zuwa shekarar 1998 lokacin da ya rasu.

Shugaba Muhammadu Buhari ya sha alwashin kawar da cin hanci da rashawa a Najeriya kuma ya bukaci Biritaniya da Amurka su taimaka masa wajen kwato kudaden sata.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here