EFCC Ta Gurfanar Da Tompolo A gaban kuliya

0
1058

Rabo Haladu Daga Kaduna Hukumar yaki da cin hanci da rashawa EFCC za ta gurfanar da tsohon
madugun \’yan gwagwarmayar yankin Neja
Delta, Government Ekpemupolo wanda ake
kira Tompolo a gaban kuliya.
Kakakin EFCC, Wilson Uwujaren a cikin wata
sanarwa,daya fitar a Abuja, ya ce Tompolo da tsohon shugaban
hukumar NIMASA, Patrick Akpobolokemi za su
bayyana gaban babbar kotun tarayya a Lagos
ne, bisa tuhumarsu kan laifuka 40.
Ana zarginsu da halarta kudaden haramun da
sata da kuma karkatar da kudaden gwamnati.
Za su bayyana gaban kuliya ne tare da wasu
mutane hudu da kamfanoni hudu.
Zarge-zargen da ake tuhumarsu a kai sun hada
da karkatar da Naira biliyan 34 a wata
yarjejeniya da hukumar NIMASA ta kulla
tsakaninta da kamfanin Global West Vessel
Specialist Limited.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here