Kotu ta bayar da belin Metuh

0
1264

Daga Usman Nasidi

Wata babbar kotu a Abuja ta bayar da belin mai magana da yawun jam\’iyyar PDP, Olisa Metuh, a kan kudi naira miliyan 400.

An kuma umarci Mista Metuh da ya mika fasfo dinsa, an kuma tilasta masa gabatar da mutane biyu wadanda za su tsaya masa, kowannensu zai biya naira miliyan 200.

Dole dai wadannan mutane biyu su kasance suna da kadara a gundumar Maitama da ke Abuja, babban birnin kasar.

A ranar Talata ne aka gurfanar da Mista Metuh a gaban kotu da ankwa a hannunsainda ake tuhumar Mista Metuh da karbar naira miliyan 400 daga hannun Kanar Sambo Dasuki, a cikin kudin makamai da ake zargin ya karkatar da su.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here