kotu ta bukaci a mika mata sambo Dasuki

0
1465

Rabo Haladu Daga Kaduna
Wata kotun tarayya da ke birnin Abuja ta umarci lauyoyin gwamnatin
tarayya da su tabbata an kai tsohon mai
bai wa shugaban kasar shawara kan
harkokin tsaro Kanar Sambo Dasuki kotu a
zaman da za a yi na gaba don ci gaba da yi
masa shari\’a.
Kotun — karkashin jagorancin mai sharia
Adeniyi Ademola — ta bayar da umarnin ne a
zamanta na ranar Laraba, sakamakon rashin
kawo Kanar Dasuki a gabanta.
Lauyoyin da ke kare Kanar Dasuki dai sun ce
jami\’an tsaro sun hana iyalinsa ganawa da shi.
Kotun ta kuma sanya ranar goma sha shida ga
watan Fabrairu domin yanke hukunci kan
bukatar gwamnatin tarayya ta a gudanar da
shari\’ar Kanar Dasuki cikin sirri, ko da ya ke
lauyoyinsa na adawa da hakan.
Ana tuhumar Kanar Dasuki ne da laifin
mallakar makamai ba bisa kaida ba, da kuma
halatta kudaden haram.
Sambo Dasuki na fuskantar wasu shari\’iun a
gaban wasu kotunan na daban, bisa zargin sace
kudaden da suka kai $2.1bn wadanda aka ware

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here