IMRANA ABDULLAHi daga kaduna
Sakamakon matsalar da aka samu a game da cutar Lassa da make samu daga berate lamarin ya haifar da samun tsadar maganin bera musamman a duk fadin arewacin kasar baki daya.
Rahotannin da muke samu daga kasuwannin da ake had a hadar saye da sayarwa da ke cikin jahar Kano na nuni da cewa maganin kashe beraye ya yi tashin gwauron zabi sakamakon iron tsananin bukatar da ake yi wajen sayen maganin.
In dai za a iya tunawa kamar yadda aka sani a yan kwanakinnan da akwai tsananin fargabar da ke haifar da tashin hankali ga daukacin jama ar Najeriya,sakamakon irin yadda ake samun matsalar cutar zazzabin Lassa da bera ko beraye suke haddhad dashesasawa musamman irin yadda cutar ke kai jama a Lahira ba tare da bata lokaci ba.
Lamar yadda wakilinmu ya yi wani Dan gajeren bincike ya gano irin yadda wadansu mutane ke fama da barazanar kamuwa da wannan cuta sakamakon irin yadda beraye manya manya suke kai kawo a cikin gidajensu tsawon lokaci.Sai kuma ga shi a yanzu lamarin bera na kara zama hadari a tarayyar Najeriya.