Rabo Haladu Daga Kaduna Gwamnatin jihar Kano
ta yi wa wasu barayin shanu afuwa, bayan
da suka ce sun tuba da satar.
Mutane 39 da ke yankin Gomo a karamar
hukumar Sumaila ne suka mika wuya ga
hukumomin, wadanda kuma aka yi musu afuwa
a wani biki da aka gudanar a yankin nasu.
Kwamishinan \’yan sandan jihar Kano,
Muhammad Musa Katsina, ya ce sun bai wa
barayin shanu a jihar zabi — ko dai su mika
wuya ko kuma a bi su cikin daji a kama su.
Kusan dukka wadanda aka yi wa afuwar suna
cewa sun mika wuya ne saboda tsoron Allah da
kuma ganin satar shanun hanya ce ba mai
bullewa ba.
Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na jihar ya
ce daya daga cikin sharuddan da aka gindaya
wa barayin da suka tuba, shi ne ba za su sake
komawa aikata kowanne irin babban laifi ba.
Hukumomi dai a jihar Kano na fatan wannan
mataki na tuba da wasu satar shanu a Kano su
ka yi zai taimaka wajen karya kashin-bayan
masu satar shanu a jihar, kasancewar da dama
daga wadanda suka tuba din, gawurtattun
barayi ne da suka addabi jihar.
Masu sharhi dai na fatan mutanen sun tuba ne
har zuci, inda suka ce Allah ya sa ba tuban
muzuru ba ne.