An Yi Wa Matar Aure Yankan Rago

0
1298

Daga Usman Nasidi

A makon daya gabata ne wasu mutane da ba a san ko su wane ne ba, suka shiga wani gida inda suka yi wa wata matar aure mai suna A’isha
Aliyu yankan rago a Unguwar Bachirawa da ke karamar Hukumar Fagge a Jihar Kano.

Bayanai sun ce mutanen sun kashe marigayiya A’isha Aliyu mai kimanin shekara 19 ta hanyar yanka mata wuya, kuma ba su dauki komai a gidan ba.

Mijin marigayiyar Malam Abdullahi Sani ya bayyana cewa ya koma gidansa da ke Unguwar Bachirawa a shekaranjiya Laraba da misalin karfe 8:30 na dare inda ya iske matarsa A’isha kwance cikin jini male-male.

Ya ce marigayiyar babu wasu alamu da za su nuna cewa wadanda suka kashe matar tasa sun yi mata fyade kafin kisan.

Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Kano, DSP Magaji Musa Majiya ya tabbatar da faruwar lamarin inda ya ce tuni jami’ansu suka shiga bincike don gano wadanda ke da alhakin kisan matar.

Majiya ya ce za su fadada bincike har zuwa ga makwabtan marigayiyar, domin “Akwai mamaki kwarai a ce an kashe mutum a farko-farkon dare ba tare da makwabta sun ji wani motsi ba,” inji shi.

An yi jana’izar marigayiyar kamar yadda addinin Musulunci ya tanada bayan likitoci sun tabbatar da rasuwarta.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here