Rabo Haladu Daga Kaduna \’Yan Nigeria suna ci gaba da mayar da
martani kan karin farashin kananzir da
gwamnati ta yi.
A wannan makon ne dai gwamnati
ta sanar da karin Naira 33 a kan kowace lita,
ma\’ana ta tashi daga Naira 50 zuwa naira 83.
Alhaji Bashir Dan Malam shi ne shugaban
kungiyar masu gidajen Mai masu zaman kansu
wato IPMAN a jihar Kano, ya shaidawa manema labarai
cewa karin farashin ba shi da wata illa
matukar za a samar da shi a duk fadin kasar.
To sai dai Alhaji Lawal Muhammad Dan Zaki na
kungiyar ta IPMAN na ganin karin bashi da
wata fa\’ida, idan aka yi la\’akkari da karin da
aka dade ana yi a kan man Fetur da shi
Kananzir, amma har yanzu bai wadata a kasar
ba.