saraki ya mayar wa da obasanjo martani

0
1348

Rabo Haladu Daga Kaduna Shugaban majalisar dattawa
Abubakar Bukola Saraki ya mayar da
martani ga tsohon shugaban kasar
Olusegun Obasanjo, kan batun wasikar da
ya aika majalisun dokokin kasa
A cikin wasikar, Obasanjo ya zargi \’yan
majalisar dokoki da cin hanci da kuma
almubazzaranci da dukiyar kasa duk da irin
mummunan yanayin da tattalin arzikin Najeriya
ke ciki.
Obasanjo ya zargi sanatoci da \’yan majalisar
wakilai da tsara wa kansu albashi da alawus-
alawus fiye da abin da hukumar tara kudin
shiga da raba shi da kuma tsara albashi da
hakkokin ma\’aikata ta kasa (RMAFC), ta
kayyadewa \’yan majalisar.
A martaninsa ta shafinsa na Twitter, Saraki ya
godewa tsohon shugaba Obasanjo, sannan
kuma ya jaddada cewa majalisun dokokin kasar
karkashin jagorancinsa, na mayar da hankali
wajen shugabanci nagari da adalci da kuma yin
aiki a bayyane ta yin la\’akari da yanayin
tattalin arzikin kasar.
Saraki ya kara da cewa a yanzu majalisar ta
bullo da wasu sauye-sauye kan yadda ake
kashe kudin majalisun dokokin kasar.
Sabanin da da yan majilasun kasar kanyi wakaci waka tashi da dukiyar Nijeriya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here