shirin ciyar da dalibai zai bunkasa Ilimi-jatau

0
1663

Isah Ahmed Daga Jos

Maqaddashin shugaban qaramar hukumar Lere da ke jihar Kaduna Mista
Sunday Jatau ya bayyana cewa babu shakka shirin nan na baiwa xaliban
makarantun firamare abinci kyauta da gwamnatin jihar Kaduna ta
qirqiro, wanda ake gudana da shi a halin yanzu zai bunqasa ilmi a
jihar. Mista Sunday Jatau ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa
da \’yan jarida, a garin Saminaka.

Ya ce wannan shiri yana da kyau kwarai da gaske domin ya qarfafawa
iyaye gwiwa wajen tura \’yayansu zuwa makarantu.

\’\’A gaskiya akwai nasara kan wannan shiri a qaramar hukumar Lere,
domin shirin yana tafiya daidai kamar yadda aka tsara shi, duk da
\’yan matsalolin da aka samu. Kuma baya ga samar da ayyukan yi ga masu
dafa abincin da aka xauka aiki, masu sayar da kayayyakin abinci suna
samun kasuwa a wannan yanki, sakamakon fara gudanar da shirin\’\’.

Ya yi kira ga iyayen yara kan su baiwa wannan shiri goyan baya da
haxin kai, domin a cigaba da samun nasarar da aka fara samu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here