Daga Usman Nasidi
Hukumar bayar da agajin gaggawa ta kasar Najeriya, NEMA ta ce akalla mutane takwas ne suka mutu a harin da wasu \’yan kunar bakin wake suka kai a jihar Adamawa ranar Juma\’a.
Babban jami\’in hukumar da ke kula da arewa maso gabashin kasar, Alhaji Muhammad Kanar,ya shaida cewa mutane 28 suka jikkata a harin, wanda aka kai a wata kasuwa da ke garin Gombi.
A cewarsa, cikin wadanda suka mutu har da \’yan kunar bakin waken guda biyu. Ya kara da cewa tuni aka kai wadanda suka jikkata asibiti domin kulawa da su.
Ganau sun shaida cewa \’yan kunar bakin waken sun tayar da bama baman da ke jikinsu ne a lokacin da kasuwar ke cike makil da jama\’a.
A shekarar 2014 ne dakarun sojin Najeriya suka kwato garin na Gombi daga hannun \’yan kungiyar Boko Haram. Sai dai tun daga wancan lokacin \’yan kungiyar ta Boko Haram ke yunkurin sake kwace shi.
Kazalika, labaran da ke fitowa daga Bargaram a kasar Kamaru ma sun tabbatar da cewa an kai harin hare-haren kunar bakin wake uku a garin.
A yanzu haka dai an bayyana cewa mutane biyar ne suka hallaka a yayin da wasu biyu kuma suka ji rauni. Sai dai kuma dukkanin layukan sadarwa na garin na fuskantar matsala.