an karya lagon yan boko haram-fadar shugaban kasa

0
1300

Rabo Haladu Daga Kaduna
Fadar shugaban kasa ta ce harin da
mayakan Boko Haram suka kai a kauyen
Dalori da ke kusa da birnin Maidugur,i
wanda ya hallaka mutane masu dimbin
yawa, ba zai kawar da maganar da
shugaban kasar ya yi cewa sojojin kasar sun
karya-lagon kungiyar ba.
Kakakin fadar shugaban kasar Malam Garba
Shehu ya ce \’yan kungiyar ta Boko Haram sun
kai wannan harin ne a kokarin da suke yi na
shigowa garuruwa domin su buya saboda irin
yadda sojoji ke fatattakarsu daga dajin
Sambisa.
Malam Garba Shehu ya ce wannan lamari da ya
faru ya yi wa shugaban kasa Muhammadu
Buhari ciwo, sannan ya aika da sakon ta\’aziyya
da jaje ga iyalan mutanen da wannan hare-hare
ya rutsa da su.
Kakakin fadar shugaban kasar ya ce ya kamata
mutane su kasance masu sanya ido a kan duk
wani mutum da suka ga ba su yarda da shi ba,
sannan a rinka kula a dukkan wajen da ake
taruwar jama\’a na irin mutanen da ke wajen
domin gujewa sake faruwar wannan lamari.
Wadannan hare-hare dai na zuwa ne a daidai
lokacin da jami\’an sojin Nigeria ke ikirarin
kary- lagon \’yan Boko Haram din a yankin
arewa maso gabashin Nijariya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here