Daga Usman Nasidi
’Yan sanda sun kama wadansu matasa bisa zarginsu da yunkurin yin fyade ga wata matar aure a Unguwar Dabai a karamar Hukumar Gwale da ke Jihar Kano.
Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Kano DSP Magaji Musa Majiya ya ce an kama Anas mai shekara 14 da Umar mai shekara 13 a ranar Litinin da ta gabata, lokacin da suka yi yunkurin yi wa wata mace mai shayarwa fyade tare da kokarin yi mata sata.
Yace “Lokacin da suka shiga gidan daya daga cikinsu ya sanya mata adda a makwagoro yayin da daya ya dora wuka a wuyan jaririyar da take shayarwa suka yi barazanar yanka su matukar ba ta ba su hadin kai ba.
A daidai lokacin ne, daya daga cikinsu ya yi kokarin yi wa matar fyade, Sai dai kafin sukai ga aikata hakan, sai suka ji motsin jami’anmu da ke sintiri a unguwar suka gudu.
Bayan matar ta kai rahoto ga ofishinmu da ke yankin sai muka shiga nemansu inda muka yi nasarar kama su, kuma sun amsa laifin da ake zarginsu na yunkurin kisa da fyade da sata. Don haka da zarar mun kammala bincike za mu kai su kotu,” inji Majiya.
Matasan sun shaida cewa sun je gidan matar ce da niyyar yi mata sata sai suka tashe ta daga barci suka sanya mata wuka a wuya suka umarce ta da ta bayar da hadin kai ko kuma mu kashe ta.
Dayan daga cikinsu yace “A nan na cire wandona ina niyyar lalata da ita ne sai muka ji karar jiniyar ’yan sanda sai muka gudu. Da safe kuma sai aka kama iyayenmu inda suka kai mu wurin ’yan sanda,” inji Umar.
Anas ya ce Umar ne ya gayyace shi zuwa gidan matar kuma shi ne ya umarce shi ya dora wa jaririyar wuka a wuyanta.