Majalisar Dokokin Filato zata binciki Matsalar rashin ruwan

0
1013

Isah Ahmed Daga Jos

Majalisar dokokin jihar Filato ta kafa kwamitin da zai binciki
matsalar rashin ruwan sha da ake fama da shi, a garin Jos da kewaye.
Majalisar dokokin ta kafa kwamitin da zai binciki wannan matsala ne,
bayan da Dan majalisar dokokin jihar mai wakiltar mazabar Jos ta
Arewa maso Arewa Honarabul Ibrahim Baba Hassan ya gabatar da wannan
kuduri a gaban majalisar.

Dan majalisar ya yi bayanin cewa al\’ummar Jos da kewaye suna cikin
mawuyacin hali sakamakon wannan matsala ta karancin ruwan sha. Ya ce
wannan matsala ta faru ne sakamakon gazawar gwamnatocin da suka
gabata.

\’\’A halin da ake ciki a kullum zaka ga yara kanana da mata suna fita
daga gidajensu tun karfe hudu na asuba, don neman ruwan da zasu yi
amfani da shi a gidajensu\’\’.

Ya ce abin takaici ne ganin irin makudan kudaden da gwamnatocin baya
suka kashe tun daga lokacin da aka dawo mulkin damakoradiya zuwa
yanzu, don magance wannan matsala amma babu wani sakamako na alheri da
aka gani kan wannan matsala.

Ya yi kira ga sabuwar gwamnatin jihar Filato ta kawowa al\’ummar Jos
dauki kan wannan mawuyacin hali da suke ciki, na karancin ruwan sha.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here