Rabo Haladu Daga Kaduna
Malaman Addinin Musulinci da na Kirista a
Najeriya, na ci gaba da nuna damuwa kan
yadda wasu mutane da ake zargi matsafa
ne ke cire sassan jikin mutane domin yin
tsafi.
Malaman sun nuna damuwar ne bayan
rahotanni sun nuna yadda ake ci gaba da cire
sassan jikin mutane, inda ko da a baya bayan
nan sai da aka kwakule idanun wani karamin
yaro a garin Zariya na jihar Kaduna.
Wasu Malamai da suka zanta da manema labarai sun
bayyana cire sassan jikin mutane domin yin
tsafi da su a matsayin babban laifi.
Shekh Dahiru Usman Bauchi, wani fitaccen
Malamin addinin Islama, ya ce, \”Wanda ya
hada tsafi da gabobin mutane, to ya yi laifi
guda biyu: ya yi shirka sannan ya cuci mutanen
da ya cire sassansu. Idan aka cire hannu ko
kafa ko wani sashe na jikin mutum bayan ya
mutu, daidai yake da idan aka cire su idan
mutum yana da rai saboda dan adam yana da
alfarma.\”
Shi ma Malamin addinin Kirista, Rabaren
Shu\’aibu Bel, ya ce duk mutumin da ya cire
sassan jikin mutane domin yin tsafi da su, ba
zai gama da duniya lafiya ba.
Ya kara da cewa, \”Abin da duk mutum ya shuka
shi zai girba. A ranar lahira za a yi masa
mummunar shari\’a, kuma a duniya ma Allah
yana iya hukunta duk wani laifi; ana iya gajarta
kwamnakinmu, wani lokacin abubuwa munana
suna iya faruwa a kanmu\”.
Rabaren Shu\’aibu Bel ya ce kasashen duniyacubits
suna kallon \’yan Najeriya a matsayin masu bin
addini sau-da-kafa, sai dai halayen \’yan kasar
na cin karo da addininsu.