Alhaji Mun Ji Kumya!!

0
1554

Daga Zubair A. Sada

WANI Buzu ne dattijo ya dade yana gadi a gidan wani attajiri a Unguwar masu hannu da shuni. Alhajin yana da bene ne hawa daya, kuma saboda sabo da suka yi da Buzun nan da iyalansa duka ya ji tausayinsa ya bar su a gidansa don su sami aikin yi da na cin abinci, amma idan domin gadi ne, to da tuni ya kore shi.

Al\’adar Buzun duk safiya zai hau sama domin ya gaida Alhaji, sai su dan taba hira, kuma gogan naka ya iya shara ta. Ranar nan Alhaji da dare ya sauko ya kwashe kayan makaman Buzu ya hau bene da su. Da safe Buzu na alla-alla ya hau sama ya ba Alhaji bayani. Da ya hau suka gaisa sai ya ce\’\’ Alhaji! Jiya mutanen sun zo (yana nufin barayi), mun sha artabu da su, da kyar na kwaci kaina, sai dai sun gudu da kayan aikina..\’\’.

Sai Alhaji ya dauko kayan a bayan kujerun falonsa, ya ce\’\’ su ne wadannan?\’\’. Buzu ya fahimci kwanan zancen, sai ya yi sauri ya amsa ya ce, \’\’assha Alhaji mun ji kumya, mun ji kumya, mun ji kumya\’\’.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here