SHUGABAN kamfanin saye da sayar da motoci na \’Sabuwar A. U. Motors\’ da ke Kaduna, Alhaji Tijjani Nababa Naira Power ya yi kira da babbar murya ga hukumar kwastan ta kasa, karkashin shugabancin Kanar (mai ritaya) Hameed Ali da ya yi wa Allah ya sake duba dokar shigo da motocin hawa da ake wa lakabi da \’yan kwatano a Najeriya, sannan ya yi sauki ga harajin kwastan da za a dinga biya wa motocin, domin talaka ya samu saukin a batun sufuri ko kuma ya mallaki abin hawa cikin rahusa.
Ciyaman na A.U. Motors, Alhaji Tijjani Naira Power ya ce ko shakka babu, tsawwala wa motocin kudin \’duty\’, zai kawo karancin masu sayo motocin sannan talaka ne zai shiga tasku, domin kuwa motocin sun yi karanci ga dimbin yawan al\’ummar da ke wannan kasa wadanda ba sa iya mallakar abin hawan.
Ya kara da cewa, arzikin da Allah ya yi wa wannan kasa tamu Najeriya yana da yawan gaske ciki har da akwai yawan mutane da muke da su, sai dai abin ban takaici za ka ga motocin da suke zirga-zirgar sufuri sun yi wa dimbin jama\’ar kadan. Ya ce shugaban na kwastan, Hameed Ali haziki ne kuma mai kaunar talakawa ne, don haka ne ma shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ga dacewarsa na rike hukumar kwastan na kasar nan ya kuma nada shi.
Naira Power har ila yau ya yi kira ga shugaban na kwastan da ya cire kwastan \’duty\’ ko ya rage shi matuka na kayayyakin gwanjo da ma misalin ruwan zamzam da yawancin alhazai suke daukowa daga Makkah a yayin aikin Hajji ko Umrah. Ya ce ruwan zamzam dai magani ne shi kansa na cututtuka da damar gaske, sannan sutura kuwa irin ta gwanjo, suturta al\’aura ce a yankin Arewacin Najeriya cikin sauki kuma tabbatar da tsafta ce.
Daga karshe Ciyaman na A.U Motors din ya yi addu\’ar Allah Ya sa shugabanninmu su ji tausayinmu, don su ma Allah Ya ji tausayinsu ya shige masu a gabansu ga dukkan abin da suka sanya a gaba.