Rabo Haladu Daga Kaduna Faduwar farashin man fetur a duniya ta
janyo raguwar sayen manyan motoci kirar
Porsche da kimamin kashi hamsin cikin
dari.
A baya, lokacin da ake samun kudi sosai, \’yan
Najeriya masu hannu da shuni su kan sayi irin
wadannan manyan motocin.
Manajan Daraktan, kamfanin sayar da Porsche
a Lagos, Parvin Singh ya shaida wa manema labarai cewar
kasuwar motar ta fadi da kashi hamsin cikin
100 idan aka kwatanta da shekarar 2014.
A cewarsa, a yanzu attajirai sun kauracewa
kamfanin saboda farashin mai ya fadi a duniya.
Man fetur ne ke samar da kashi saba\’in cikin
dari na kudaden shigar gwamnatin Najeriya,
kuma idan gwamnati ta dakatar da kashe kudi,
to hakan na matukar tasiri ga \’yan kasuwa
masu zaman kansu a kasar.