Rabo Haladu, Daga Kaduna
FADAR shugaban kasa ta ce harin da mayakan Boko Haram suka kai a kauyen
Dalori da ke kusa da birnin Maiduguri wanda ya hallaka mutane masu dimbin
yawa, ba zai kawar da maganar da shugaban kasar ya yi cewa sojojin kasar sun
karya kadarin kungiyar ba.
Kakakin fadar shugaban kasar, Malam Garba Shehu ya ce \’yan kungiyar ta Boko Haram sun
kai wannan harin ne a kokarin da suke yi na shigowa garuruwa domin su buya saboda irin
yadda sojoji ke fatattakarsu daga dajin Sambisa.
Malam Garba Shehu ya ce wannan lamari da ya
faru ya yi wa shugaban kasa Muhammadu Buhari ciwo, sannan ya aika da sakon ta\’aziyya
da jaje ga iyalan mutanen da wannan hare-hare ya rutsa da su.
Kakakin fadar shugaban kasar ya ce ya kamata mutane su kasance masu sanya ido a kan duk
wani mutum da suka ga ba su yarda da shi ba, sannan a rinka kula a dukkan wajen da ake
taruwar jama\’a na irin mutanen da ke wajen domin gujewa sake faruwar wannan lamari.
Wadannan hare-hare dai na zuwa ne a daidai lokacin da jami\’an sojin Nijeriya ke ikirarin
karya kadarin \’yan Boko Haram din a yankin arewa maso gabashin Nijeriya.