kama dillalan miyagun kwayoyi a Kaduna

0
1102

\"kano-state-logo\"Rabo Haladu Da IMRANa ABDULLAHi rDaga Kaduna
Hukumar hana sha da fataucin miyagun
kwayoyi a Najeriya, NDLEA shiyyar Kaduna
ta ce ta kama wasu masu sha da kuma
fataucin miyagun kwayoyi su 25 a jihar.
Hukumar ta nuna wa manema labarai wasu
tarin kwayoyi ciki har da hodar iblis, watau
Cocaine da kuma tabar wiwi da ta ce ta kwace
su ne daga hannun dillalan kwayoyi a jihar.
Gwamnatin jihar Kaduna dai na cewa a kokarin
magance tafka manyan laifuffuka ne ta hada
gwiwa da hukumar NDLEA, abin da ya haifar da
wannan kame.
A watan da ya wuce ma, a jihar Kano da ke
makwabtaka da Kaduna, rundunar \’yan sanda a
jihar ta ce ta kwato miyagun kwayoyi da suka
kai Naira biliyan daya da miliyan dari 200 a
cikin watanni biyu da suka wuce.
Rundunar ta ce ta kuma yi nasarar kama
dillalan kwayoyi, ciki har da masu sayar da
hodar ibilis.

 

 

 

 

Shugaban hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi na jahar kaduna mistake Samuel Aziege,ya kuma godewa gwamnatin jahar kaduna visa iron tallafin motocin gudanar da aikin da ta basu,India ya bayyana lamarin a matsayin abin da zai ba su damar aiki babu kama hannun yaroyaro domin tsaftace jahar daga masu sha da kuma sayar da miyagun kwayoyiva jahar baki daya.
Da wakilinmu take jin ta bakin wash da aka kama bisa sha ko sayar da miyagun kwayoyi sun bayyana nadamar gudanar da ayyukan da suke yi tare da alkawarin cewa za su daina baki daya.
Sai dai shugaban hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyin jahar kaduna ya ce za su gurfanar da wadanda suka kama gaban kuliya.
Ya ce sun kama masu wannan aikin ne a marabar Rido,sabon tasha,Gadar Kawo,Kasuwa da tashar mota da sauran wuraren da suka lashi takobin tsarkake jahar daga masu wannan aikin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here