garimare ya fado a indiya har ya kashe sojoji 10

0
1025

Sojoji 10 ne suka mutu sakamakon fadowar gajimare
jihar KAshmir ta kasar Indiya.
Kamfanin dillancin labarai na Indiya ya sanar da cewa,
a kwanaki 2 da suka gabata an bayar da labarin cewa,
sojojin sun bata a yankin Ladakh mai dusar kankara,
inda kuma daga baya aka tabbatar da mutuwarsu
bayan gane cewa, gajimare ne ya fado tare da yin
ajalinsu.
Firaministan Indiya Narendra Modi ya mika sakon
ta\’aziyyarsa game da mutuwar sojojin.
Fadowar gajimare da zaftarewar kasa na yawan
afkuwa a yankin Kashmir, inda kuma sakamakon rikicin
Pakistan da Indiya aka kai sojoji yankin wanda ke
gabas da dutsen Himalaya.
A watan da ya gabata ma gajimare ya fado a yankin
inda sojoji 4 suka mutu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here