Rabo Haladu, Daga Kaduna.
SHUGABAN kasa Muhammadu Buhari ya shaida wa manema labarai cewa ba zai yarda \’yan damfarar da ke amfani da sunan Boko-Haram su yaudare shi ba.
Shugaban ya yi wadannan kalaman ne a hirarsa da manema labarai a birnin London, bayan ya hallaci taron neman agaji ga \’yan gudun hijirar Syria.
Shugaba Buhari ya bayyana haka ne bayan da wasu mutane ke fitowa suna cewa za su shiga tsakanin gwamnati da Boko-Haram domin a saki \’yan matan Chibok sama da 200 wadanda ake zargin kungiyar ta ‘yan boko-haram ta sace su tun cikin shekarar 2014.
Shugaba Buhari ya kara da cewa tattalin arzikin kasar nan ya fada mawuyacin hali ne saboda faduwar da farashin man fetur ya yi a kasuwannin duniya.
Sai dai ya ce gwamnatinsa tana duba wasu hanyoyin domin samun kudin shiga.
Shugaba Buhari ya ce ba zai rage darajar Naira, ba, yana mai cewa babu wata shaida da ke nuna cewa tattalin arzikin kasa, zai bunkasa idan aka rage darajar naira.