Rabo Haladu, Daga Kaduna.
FITACCEN mawakin nan na Hausa a Najeriya, Alhaji Sani Dan-Indo, ya rasu.
Wasu makusantan mawakin sun shaida wa manema labarai cewa Sani Dan-Indo, ya rasu ne a birnin Kano.
Mawakin, wanda ya rasu yana da shekara 55 a duniya, ya bar mata daya da \’ya\’ya shida.
Zubairu, daya daga cikin \’ya\’yan margayin ya ce sun rabu lafiya da daddare a ranar Lahadi,
amma kuma da asuba a ranar Litinin, Allah ya dauki ransa.
Marigayi Sani Dan Indo ya yi wakoki da dama a fannoni daban-daban da suka hada da noma da al\’ada da kuma zamantakewa wadanda suka yi fice a kasar Hausa.
Daga cikin wakokinsa akwai \”Dan-Indo Mutumin Gaskiya\”, wacce ta shahara sosai.
A shekarar 2011 ya samu sabani da hukumar tace fina-finai ta jihar Kano, saboda ya yi wasu
wakoki da hukumar ta ce ba su dace ba, kuma hakan ya sa aka yanke masa hukuncin daurin
wata shida a gidan kurkuku. Allah Ya jikansa, ya ba da hakurin rashi.