mawaki sani dan indo ya rasu

0
2030

Rabo Haladu Daga Laduna Fitaccen mawakin nan na Hausa a
Najeriya, Alhaji Sani Dan-Indo, ya rasu.
Wasu makusantan mawakin sun shaida wa manema labarai
cewa Sani Dan-Indo, ya rasu ne a birnin Kano.
Mawakin, wanda ya rasu yana da shekara 55 a
duniya, ya bar mata daya da \’ya\’ya shida.
Zubairu, daya daga cikin \’ya\’yan margayin ya
ce sun rabu lafiya da daddare a ranar Lahadi,
amma kuma da asuba a ranar Litinin, Allah ya
dauki ransa.
Marigayi Sani Dan Indo ya yi wakoki da dama a
fannoni daban-daban da suka hada da noma da
al\’ada da kuma zamantakewa wadanda suka yi
fice a kasar Hausa.
Daga cikin wakokinsa akwai \”Dan-Indo
Mutumin Gaskiya\”, wacce ta shahara sosai.
A shekarar 2011 ya samu sabani da hukumar
tace fina-finai ta jihar Kano, saboda ya yi wasu
wakoki da hukumar ta ce ba su dace ba, kuma
hakan ya sa aka yanke masa hukuncin daurin
wata shida a gidan kurkuku.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here