SEMA Ta Yi Wa Yara 70 Kaciya A Sansanin ’Yan Gudun Hijira

0
1411

Daga Usman Nasidi

HUKUMAR bayar da Tallafin Gagggawa ta Jihar Yobe (SEMA) ta yi kaciya ga yara 70 a sansanin ’yan gudun hijirar da ke Pompari a garin Damaturu.
An gudanar da kaciyar ce a karkashin wani bikin gargajiya da ake yi wa lakabi da FANFARE da kabilar Kanuri ke gudanar da shi a lokacin hunturu.
Jami’an kiwon lafiya ne suka gudanar da kaciyar tare da halartar iyayen yaran da jami’an Hukumar ta SEMA.
Da yake bayani bayan kammala kaciyar, Babban Sakataren Hukumar SEMA, Alhaji Musa Idi Jidawa ya ce, an gudanar da kaciyar cikin nasara, kuma hukumar ta yanke shawarar gudanar da kaciyar ce don tallafa wa ’yan gudun hijirar wajen yi wa ’ya’yansu kaciya.
Hakazalika, Hukumar ta ba da kayan sawa da faranti guda na abinci dauke da naman kaza ga kowane yaron da aka yi wa kaciya.
A wani labarin makamancin wannan, Hukumar SEMA ta ba da tallafin kayan amfanin yau da kullum ga wasu ’yan gudun hijira a sansanonin Kasaisa da Bukar Ali kusa da garin Damaturu.
Kayayyakin da aka rarraba sun hada da tantuna 100 da turamen atamfa 100 da katifu 50. Jami’in da ke kula da sansanin Kasaisa Bukar Ali Ibn El-Kanemi ne ya karbi kayayyakin a madadin ’yan gudun hijirar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here