0
1636

An Tube Mai Unguwa Kan Yi Wa Budurwa Ciki

Daga Usman Nasidi

MASARAUTAR Dutse da ke Jihar Jigawa ta tube Mai unguwar Chaichai mai suna Mai unguwa Danjummai da ke masarautar bayan an zarge shi da yi wa wata budurwa ciki.
Mutanen yankin Chaichai sun jima suna zargin mai unguwar da neman mata, kuma dubunsa ya cika ne lokacin da aka samu labarin ya yi wa wata yarinya ciki ta haifa masa tagwaye ana shirin rada wa yaran suna.
Wata majiyar ta bayyana cewa Mai unguwa Danjummai ya amsa laifin da ake zarginsa da shi, inda ya bukaci a rufa masa asiri tare da yin alkawarin ba zai sake aikata haka ba.
Budurwar wadda aka sakaya sunanta, bayanai sun nuna cewa, mai unguwar ya jima yana lalata da ita da wasu ’yan mata a yankin amma aka rasa yadda za a yi da shi.
Majiya mai tushe a fadar Sarkin Dutse ta shaida cewa Hakimin yankin Chaichai, Alhaji Zaharaddini Muhammed Sunusi ya ce masarauta tana sane da abin da mai unguwar ya aikata, kuma tuni Hakimin ya tube mai unguwar daga sarauta kuma za a dauki matakin ladabtar da shi domin hakan ya zama darasi ga saura.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here