An tube Mai Unguwa Kan Yi Wa Budurwa Ciki

0
2102

Daga Usman Nasidi

Masarautar Dutse da ke Jihar Jigawa ta tube Mai unguwar Chaichai mai suna Mai unguwa danjimmai da ke masarautar bayan an zarge shi da yi wa wata budurwa ciki.

Mutanen yankin Chaichai sun jima suna zargin mai unguwar da neman mata, kuma dubunsa ta cika ne lokacin da aka samu labarin ya yi wata yarinya ciki ta haifa masa tagwaye ana shirin rada wa yaran suna.

Wata Majiyar ta bayyana cewa Mai unguwa Danjimmai ya amsa laifin da ake zarginsa inda ya bukaci a rufa masa asiri tare da yin alkawarin ba zai sake aikata haka ba.

Budurwar wadda aka sakaya sananta bayanai sun ce mai unguwar ya jima yana lalata da ita da wasu ’yan mata a yankin amma aka rasa yadda za a yi da shi.

Majiya mai tushe a fadar Sarkin Dutse ta shaida mana cewa sarkin Chaichai Alhaji Zaharaddini Muhammed Sunusi ya ce masarauta tana sane da abin da mai unguwar ya aikata, kuma tuni hakimin ya tube mai unguwar daga sarauta kuma za a dauki matakin ladabtar da shi domin hakan ya zama darasi ga saura.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here