Rabo Haladu, Daga Kaduna.
GWAMNAN jihar Borno Kashim Shettima, ya ce babu wata karamar hukuma a jihar da ke hannun
Boko Haram.
Gwamnan ya bayyana haka ne bayan wasu rahotanni sun ambato wani dan majalisar dattawa daga jihar da kuma wasu mazauna jihar na cewa \’yan kungiyar ta Boko Haram suna rike da wasu kananan hukumomi.
Wannan lamari dai ya tayar da jijiyoyin wuya, musamman bayan ikirarin da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi a kwanakin baya cewa gwamnatinsa ta murkushe kungiyar ta Boko Haram, yadda ba za ta iya kwace garuruwa daga hannun sojoji kamar yadda ta yi a wasu lokuta na baya ba.
Gwamna Shettima ya shaida wa manema labarai cewa an samu matukar ci gaba a yakin da ake yi da kungiyar ta Boko Haram, yana mai cewa ko da ya ke ya yarda \’yan kungiyar suna rike da wasu yankuna a wasu kananan hukumomin, amma ba sa rike da wata karamar hukuma kacokan.
Ya ce, \”A iyaka sanina babu karamar hukuma daya da ke hannu \’yan Boko Haram, amma \’yan kungiyar suna nan jefi-jefi a cikin jeji. Inda ma zan ce suna das karfi shi ne watakila a kananan hukumomin Abadam, da Mabar da
Kalabalge. A can din ma ba wai sun rike kananan hukumomin ba ne, suna warwatse a wasu yankuna ne kawai amma ba kananan hukumomi ba kamar yadda wasu mutane ke fada ba\’\’.