An Kama Sojojin Da Suke Safarar Makamai

0
1308

Rabo Haladu, Daga Kaduna.

RUNDUNAR sojin Nijeriya ta ce ta kama wasu sojojinta da ake zargi da yunkurin sayar da makamai ga \’yan kungiyar Boko Haram a yankin arewa maso gabashin kasar.
Kakakin rundunar, Kanar Sani Usman Kuka-Sheka, ya shaida wa manema labarai cewa a ranar Lahadin da ta gabata ne aka kama biyu daga cikin sojojin a tashar mota ta Yola da wasu makamai da albarusai na soja suna neman kai wa wasu wurare hari.
Ya ce suna amfani da wata dama ta bude kasuwanni da aka yi a Borno da Yobe suna hada baki da \’yan ta\’adda suna sayar musu da makamai.
An kuma same su da gurneti mai hayaki, harsasai dubu biyu da dari da talatin da shida, da wasu harsasai na musamman guda hamsin, da kuma harsasai na bindigogi masu sarrafa kansu.
Rundunar ta ce ana ci gaba da bincike kuma nan ba da jimawa ba za a gurfanar da su a gaban kotun soji bisa zargin da ake masu, domin yanke masu hukuncin da ya kamata.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here