NLC Ta Yi Allah-wadai Da Korar Ma\’aikata A Warri

0
1195

Rabo Haladu, Daga Kaduna.

KUNGIYAR kwadago ta kasa  NLC ta yi  zanga-zanga a jihar Imo, lamarin da ya sa ayyuka suka tsaya cik a Owerri, babban birnin jihar.
Kungiyar ta yi boren ne domin nuna kin amincewa da korar wasu ma\’aikata kimanin 500 da gwamnatin jihar ta yi.
A jawabin da ya yi ga taron ma\’aikata, shugaban kungiyar NLC, Ayuba Wabba, ya ce za su rufe dukkan ofishin gwamnati da bankuna da gidajen mai saboda korar ma\’aikatan.
NLC na zargin cewa gwamnati ta dakatar tare da korar ma\’aikatan ne ba bisa ka\’ida ba. Sai dai gwamnati ta ce ta sallami ma\’aikatan wasu hukumominta 19 ne da ba su da amfani, wadanda kuma ta mika wa \’yan kasuwa domin
su tafiyar da su, saboda haka akwai yiwuwar a maida ma\’aikatan zuwa wata ma\’aikata  da ba  tasu ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here