Ta Leko Ta Koma Ga Wasu Sojoji Su 250

0
1474

Rabo Haladu, Daga Kaduna.
WASU sojoji a Najeriya na kokawa saboda korar su da suka ce hukumomin sojin Nijeriya sun yi a karo na biyu bayan \’yan watanni da dawo da su bakin aiki.
Sojojin su 250, sun fadi cewa  bayan sake dawo da su sanadiyyar yafe musu laifuffukan da suka yi  a arewa maso gabas yayin da suke yaki da Boko Haram sai ga shi an kara korarsu daga aikin na soja karo na biyu.
Sojojin suna zargin cewa laifuffukan da ya sanya aka sake korar su bai taka kara ya karya ba.
A martaninsa, Kakakin sojin Nijeriya, Kanar Sani Usman Kuka-sheka ya ce sojojin da aka kora sun gudu ne lokacin da aka bayyana musu cewa za su koma fagen yaki da Boko Haram.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here