Rabo Haladu, Daga Kaduna.
DAKARUN Nijeriya sun ce sun kama wadansu jiragen ruwa biyu dauke da danyen mai da kuma man gas da suka yi zargin cewa na sata ne a yankin Naija-Delta da take da arzikin mai.
Wata sanarwa da rundunar hadin gwiwa ta JTF ta fitar dauke da sa hannun kakakinta, Isa Ado, ta ce ana gudanar da bincike a kan jirgin \”African Sky\” da ke dauke da tan 670 na danyen mai na sata.
An kuma kama wani jirgin ruwan mai suna \”Eucharia 111\” dauke da man gas, wanda aka ajiye a kusa da wani wuri da ake satar mai.
Haka kuma sanarwar ta kara da cewa dakarun Najeriyar sun lalata wadansu wuraren da ake satar danyen mai da man gas a jihohin Bayelsa da kuma Delta duka a yankin na Naija-Delta.
A cewar JTF, sojoji sun kama wadansu mutane bakwai da suke zargi da hannu a satar danyen man da gas da kuma ayyukan fashi a cikin teku.
Najeriya dai na asarar Biliyoyin Naira ta hanyar satar danyen mai.