Binciken Mu Ya Tabbatar Mutane 275 Ba Yan Boko Haram Ba Ne – Sojoji

0
1014

Rabo Haladu Daga Kaduna
Rundunar sojin Najeriya ta mika mutane
275 ga gwamnatin jihar Borno, wadanda
aka kama tun farko bisa zarginsu da
kasancewa \’yan Boko Haram.
An mika wa gwamna Kashim Shettima mutanen
ne bayan da sojoji suka tantance su, aka
tabbatar basu da hannu a ayyukan ta\’addanci.
Kakakin gwamnan Borno, Malam Usman Kumo
ya shaida wa manema labarai cewa daga cikin wadanda
aka sako har da \”maza 142 da mata 49 da
kuma kananan yara maza da mata su 77\”.
Kumo ya kara da cewa \” A yanzu an kai
mutanen wurin koyan sana\’o\’i, daga bisani za a
basu jari domin dogaro da kansu bayan sun
kammala koyon sana\’ar.\”
Gwamnatin jihar Borno ta kuma ce kananan
yaran za a saka su a makaranta domin su samu
ingantacciyar rayuwa.
A cikin watan Satumbar bara ma, sai da
rundunar sojin kasar ta sako wasu mutane 128
inda ta mika su ga gwamnatin jihar Borno
bayan ta tabbatar basu da alaka da kungiyar
Boko Haram.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here