An Yi Wa Yarinya Yankan Rago A Kano

0
1649

Daga Usman Nasidi

A ranar Litinin da ta gabata ne jama’ar Unguwar Bachirawa ’Yan Katako a birnin Kano suka tashi da alhinin iske gawar wata yarinya mai suna Rumasa’u Nasir wadda aka tsince ta cikin jini face-face a gefen hanya.

Rahotanni sun ce an tsinci gawar marigayiya Rumasa’u wadda aka yi wa yankan rago inda kuma aka rufe kanta da baqar leda.

Tun safiyar ranar iyayen Rumasa’u mai kimanin shekara bakwai suka neme ta suka rasa, inda suka shiga nemanta a gidajen ’yan uwa da abokan arziki, kafin daga bisani su samu labarin gano gawarta a gefen hanya.

Mahaifin marigayiyar Malam Nasir ya bayyana cewa tsawon wunin ranar ba a san inda yarinyar ta shiga ba, lamarin da ya sa suka yi ta nemanta har zuwa lokacin da aka sanar da su wanann mummunan labari.

“Da farko mun dauka bacewa ta yi, sai daga baya muka ga abin da ya fru da ita. Babu abin da zan ce, sai dai in yi mata addu’a Allah Ya jiqanta kuma Ya tona asirin wadanda suka aikata wannan mummunan abu,” inji shi.

Kakakin Rundunar ’Yan sndan Jihar Kano DSP Magaji Musa Majiya ya tabbatar da faruwar lamarin inda ya ce bayan an sanar da su labarin tsintar gawar yarinyar sun dauke ta sun kai ta asibiti don yi mata gwaje-gwaje, kuma binciken likitoci ya nuna ba a yi mata fyade ba kafin a kashe ta.

Majiya ya qara da cewa: “Kwamishinan ’Yan sandan Jihar ya bayar da umarnin a fara gudanar da bincike kan faruwar lamarin. Kuma muna kira ga duk wanda yake da wani labari game da wadanda suka aikata wannan aika-aika ya sanar da rundunarmu, don ganin an gurfanar da su a gaban shari’a.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here