Shugaban Kasa Buhari Ya Kori Shugabannin Wasu Ma\’aikatu

0
1406

Daga Usman Nasidi

GWAMNATIN Najeriya ta kori shugabannin ma\’aikatun gwamnatin tarayya guda ashirin da shida.

Da farko dai wata sanarwa da Mista Segun Adeyemi, kakakin ministan watsa labarai, Alhaji Lai Mohammed, ya fitar ranar Litinin ta ce an kori shugabannin gidan talabijin na gwamnatin tarayya, (NTA), da Federal Radio Corporation of Nigeria (FRCN), da muryar Najeriya, da kamfanin dillacin labarai na kasar (NAN), da hukumar sa idanu a kan kafafen watsa labarai na kasar da hukumar wayar da kan jama\’a ta kasar (NOA).

Mutanen da aka kora su ne Mista Sola Omole (NTA), Malam Ladan Salihu (FRCN), Mista Sam Worlu (VON), Mista Mike Omeri (NOA), Mista Emeka Mba (NBC), Mista Ima Niboro (NAN). Sai kuma wata sanarwa da ta fito daga fadar shugaban kasar, wacce ta sanar da korar shugabannin ma\’aikatu 20.

Ma\’aikatun su ne: Hukumar kula da rarar man fetur (PTDF) Hukumar da ke sa ido kan hada kan kasashen Afirka (NEPAD), Asusun samar da Inshora na Najeriya (NSITF), Hukumar tabbatar da ka\’ida wajen sayar da kayayyakin Najeriya (NCDMB).

Hakazalika, da shugaban Bankin bayar da rancen sayen gidaje (FMBN), Asusun tallafa wa manyan makarantu (TETFund), Hukumar bunkasa fassarar sadarwa ta Najeriya (NITDA), Asusun daidaita farashin man fetur (PEF).

Sai Shugaban Hukumar kula da jiragen kasa (NRC), Hukumar da ke sa ido a harkokin saye-saye na gwamnati(BPP), Hukumar cefanar da kaddarorin gwamnati (BPE), Hukumar kula da kayyade farashin man fetur (PPPRA), Hukumar da ke sa ido kan ingancin kayayyaki (SON), Hukumar da ke sa ido kan ingancin abinci da magunguna (NAFDAC).

Haka kuma da shugaban Hukumar da ke neman masu zuba jari a Najeriya (NIPC), Bankin Masana\’antu na Najeriya (BOI), Cibiyar kula da ci gaban mata(NCWD), Asusun bayar da horo kan masana\’antu, Bankin da ke kula da shigowa da fitar da kayayyaki, Hukumar da ke hana fataucin mutane (NAPTIP),

Tsohon shugaban kasa dai Goodluck Ebele Jonathan ne ya nada akasarin mutanen da aka kora a yanzu a lokacin yana bisa karagar mulkin kasar nan.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here