Daga Usman Nasidi
’YAN SANDA a Jihar Nasarawa sun cafke wadansu matasa hudu da ake zargi sun kware wajen satar babura a garin Keffi da ke jihar.
Da yake gabatar da wadanda ake zargin ga manema labarai a ofishin binciken manyan laifuffuka (CID) na rundunar da ke Lafiya, Kakakin Rundunar ASP Umar Numan Isma’il ya ce wani mai suna Malam Abba da ke zaune a Unguwar Sabon Layi a garin Keffi ya kai kara ofishin ’yan sanda da ke Keffi.
Ya ce \” Abba ya bayyana masu cewa, a lokacin da yake komowa gida daga kauyen Tilla da daddare a kan sabon babur dinsa kirar \’Bajaj\’, wadanda ake zargin sun yi masa kwanton bauna suka auka masa da duka da sanduna da adduna suka kwace babur din suka bar shi a kwance rai a hannun Allah, bayan sun yi masa mummunan rauni a kansa.
ASP Umar Numan ya kara da cewa wanda aka kwace masa babur din ya farfado ne ya kai kara ofishin ’yan sanda na Keffi inda nan take DPO da ke kula da ofishin ya umarci jami’ansa da kuma wasu ’yan banga suka soma sintiri a yankin, kuma daga bisani suka yi nasarar kama wadanda ake zargin.
Ya ce wadanda ake zargin sun hada da Khalid Mohammed da Salisu Suleiman da Umaru Yusuf da Ali Adamu, kuma ya ce bincikensu ya gano wadanda ake zargin sun kware wajen yin amfani da makami suna satar babura a garin da kewaye, musamman daga ’yan acaba.
A cewarsa, sun kwato wasu, babura biyu daga wadanda ake zargin, inda ya shawarci matasan jihar su guje wa aikata laifuffuka su nemi sana’a don taimaka wa rayuwansu.