Hukumar Zabe Takammala Shirin Yin Zaben Lere

  0
  1871

  HUKUMAR zabe mai zaman kanta ta kasa reshen Jihar Kaduna ta bayyana cewa ta kammala shirin gudanar da zaben cike gurbi domin samar da dan majalisar da zai wakilci al\’ummar karamar hukumar Lere.

  Kwamishinan hukumar, Alhaji Abdullahi Kaugama ne ya tabbatar wa manema labarai hakan lokacin da ya kira taron manema labarai a ofishinsa a Kaduna.

  Kwamishina Kaugama ya ce hakika hukumarsa ta kammala komai domin gudanar da zaben cike gurbin dan majalisar jaha da zai wakilci mutanen karamar hukumar Lere.

  Ya ci gaba da cewa kamar yadda kundin tsarin mulki ya ba su dama cewa idan an samu gibi za su shirya zaben cike gurbin duk wani daga cikin yan majalisar.

  \”Mun kira taron duk masu ruwa da tsaki a harkar siyasa a Jahar Kaduna tun daga \’ya\’yan jam\’iyyu hudun da za su tsayar da \’yan takara zuwa ga kungiyar gamayyar jam\’iyyun da suke a jahar baki daya, domin bayyana masu irin shirin da muka yi da kuma tsarin da zaben zai fuskanta a ranar Asabar mai zuwa\” inji Kaugama.

  A wannan karon duk wanda zai kada kuri\’a idan an tantance shi zai jefa kuri\’arsa ne kawai kai tsaye,  ba kamar da ba in an tantance sai mutum ya je ya jira lokacin jefa kuri\’a ya dawo ya jefa.

  Da wakilinmu ya tuntubi sauran wakilan jam\’iyyun da suka halarci wannan taro a dakin taro na hukumar da ke cikin garin Kaduna sun bayyana gamsuwarsu da irin shirin da hukumar ta yi.

  LEAVE A REPLY

  Please enter your comment!
  Please enter your name here