Ba za mu taba Naira ba — Buhari

0
1177

Rabo Haladu, Daga Kaduna
SHUGABAN kasa Muhammadu Buhari, ya jaddada matsayinsa na kin rage darajar Naira.
Muhammadu Buhari ya yi wannan furuci ne a wani jawabi a wata tattaunawa ta Shugabannin Afrika a kan kasuwanci da saka jari a Sharm El Sheikh da ke Misira.
Buhari ya kuma kara da cewa Najeriya ba za ta iya gogayya da kasashe masu arzikin masana\’antu ba wadanda ke samar da kayayyakin bukatunsu kuma ke gasa a tsakaninsu ba.
Sannan ya kara da cewa Najeriya ba ta fitar da kayayyaki sai dai shigowa da komai da komaikai hatta ma har da tsinken sakace don haka bai ga dalilin da zai karya darajar Naira ba.
Sama da masu fada a ji dubu ne ke halartar taron a Misira, ciki har da shugabannin kasashen Afrika da Ministoci da kuma \’yan kasuwa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here