Rabo Haladu Daga Kaduna
WASU \’ya\’yan jam\’iyyar PDP a Jihar Borno sun koka sun ce babu yawunsu a zaben Sanata Ali Madu Shariff a matsayin sabon shugaban jam\’iyyar PDP na riko na kasa.
Shugaban reshen jam\’iyyar na Jihar Borno Alhaji Baba Basharu, ya bai wa jam\’iyyar ta kasa wa\’adin nan da ranar Laraba su kira taro ko kuma \’yan PDP na jihar su zauna su dauki
nasu mataki kan wannan al\’amari.
Tuni dai kwamitin amintattun jam\’iyyar PDP shi ma ya nisanta kansa da zaben Ali Modu Sheriff a matsayin shugaban jam\’iyyar.
Alhaji Baba Basharu, ya ce ba su da masaniya game da nadin da za a yi wa Ali Madu Sheriff, sai ji kawai suka ji an nada shi sabon shugaban jam\’iyyar PDP na kasa inda al\’umar Jihar Borno suka ce abin bai yi masu dadi ba.