Fulani Sun Koka Kan Tarbiyyar \’Ya\’yansu.

0
1248

 

Rabo Haladu Daga Kaduna
KUNGIYOYIN fulani sun koka matuka dangane da yawan tallace-tallacen da \’ya\’yan nasu suke yi a kan rariya. A cewar shugabannin kungiyoyin Fulanin tallar na zubar da kimar Fulani a idanun duniya,
haka kuma yana jefa rayuwar fulanin cikin halin tsaka-mai-wuya ta fuskar tsaro a saboda haka suka ce maimakon tallace-tallace ya kamata \’yan matan Fulanin su koma makaranta.
Ga dai abin da daya daga cikin shugabannin Fulani a kungiyar Miyetti Allah, a Jihar Kaduna, Malama Khadija Ardijo ta shaida wa  manema labarai cewa kowa ya san \’ya\’yan fulani da hazaka sai dai kuma suna cike da matsaloli na rashin wayewa,hakan ya sa suke fadawa halin tsaka mai wuya.

Sai ta ce, in Allah Ya yarda za su bi matakan da ya dace domin kawo karshen tallace-tallacen na Fulani a kan tituna, su maye makwafinsa da hanyoyin talla na zamani.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here