IMRANA ABDULLAHI Daga Kaduna
WADANSU ma aikatan da aka sallama daga aikin otal din Arewa da suka zo daga Jahohi daban-daban da ke karkashin wannan kamfani sun yi zanga-zangar lumana a garin Kaduna.
Wadannan mutane maza da mata sun yi wannan zanga-zanga ne sakamakon rashin biyansu kudin sallama daga aiki shekaru bakwai (7) bayan an sallame su daga aiki.
Su dai mutanen da suka yi magana ta bakin wakilinsu Umar Musa Galadima, inda suka koka a kan irin yadda rayuwa ke kokarin gagarar su kamar yadda suka ce matansu sun zama mazan a halin yanzu, saboda su ba sa iya daukar nauyin da ya dace su dauka.
\”A yanzu da yawanmu ba ma iya biyan kudin hayar gidajen da muke a ciki mu da iyalanmu, \’ya\’yanmu an kore su daga makarantu ga dai matsaloli kala-kala da suke addabar mambobinmu da dama\”.
Musa ya ci gaba da cewa da akwai wasunsu da suke cikin matsanancin halin rashin lafiya na hawan jini da sauran matsaloli,saboda ko a yanzu sai da suka tashi suka je wajen wasu mambobin nasu da ba su da lafiya suna kwance a asibiti.
Galadima ya ce duk lokacin da suka tuntubi mutanen da ya dace su biya su sai su ce masu ba kudin yin hakan don haka suna cikin matsaloli marasa iyaka.
Amma wani abin burgewa shi me irin yadda kamfanin NNDC da me karkashin jahohin Arewa 19 suka gina wani katafaren gini a kan titin Muhammadu Buhari a kusa da ofishinsu a cikin garin Kadina,amma ko yaushe ne za a samu hakkin wadannan mutanen har a biya su? Wakilin Gaskiya Ta Fi Kwabo zai gano mana hakan, da zarar ya gana da shugabannin otal-otal na Arewa domin jin ta bakinsu.