Rabo Haladu Daga Kaduna
TSOHON jakadan Nijeriya a Birtaniya, Sanata Dalhatu Sarki Tafida, ya ce ya yanke shawarar barin jam\’iyyar PDP ne saboda a cewarsa ta rasa alkibla.
Sanata sarki Tafida ya kara da cewa a yanzu babu wani aiki da PDP take yi, a da can dai sun yi abin a zo a gani amma yanzu sai kwaso mutanen da bai dace ba
jam\’iyyar ke yi.
Ya kuma ce jam\’iyyar PDP ba ta bai wa mutane irinsa girma, ba kuma a daukar shawarar su sai dai abin da \’ya\’yan jam\’iyyar suka ga damar yi. Sanata Tafida ya ce kawo yanzu bai shiga kowace jam\’iyya ba, yana dai yin nazari don sanin inda ya dace ya nufa.