An Dakatar Da Dagaci A Kano Saboda Lalata Da Yarinya

0
1678

Rabo Haladu Daga Kaduna
MAJALISAR masarautar Kano ta dakatar da wani Dagaci bisa zarginsa da yin lalata da wata yarinya \’yar shekara 13 gami da sanya mata cutar HIV.
Galadiman Kano kuma babban dan majalisar Sarki Alhaji Abbas Sanusi, shi ne ya dakatar da dagacin na Goron Maje a karamar hukumar
Danbatta Alhaji Musa Muhammad.
Iyayen yarinyar ne suka kai korafi hukumar Hizbah tuni bayan sun kama Dagacin da wannan ta\’asa, kuma ya amince da aikata hakan.
Darakta Janar na hukumar ta Hizbah Malam Abba Kabiru Sufi, ya shaida wa manema labarai cewa iyayen yarinyar ne suka kai musu korafi, inda
asibiti suka tabbatar da cewa yarinyar na dauke da cutar ta kanjamau.
Daga nan ne kuma aka mika dagacin zuwa fadar masarautar Kano, domin daukar mataki a  kan sa na kai sa kuliya manta sabo.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here