Ana Zarginsa Da Boye Matar Aure

0
1929

Daga Usman Nasidi

HUKUMAR Hisba ta karamar Hukumar Dala ta kama wani mutum mai suna Buhari Amadu dan asalin garin Kafur a Jihar Katsina bisa zarginsa da boye wata matar aure wadda tsohuwar budurwarsa ce mai suna Maryam Muhammad Malumfashi.
Bincike ya tabbatar da cewa wanda ake zargin Buhari Amadu ya yaudari tsohuwar budurwar tasa ce ta baro gidan mijinta mai suna Muhammad Sani ta taho Kano wurinsa. Bayan ta zo ne sai ya ajiye ta a wani gida da ke Unguwar Rijiya Hudu a karamar Hukumar Ungogo na tsawon kwana uku.
Bayanai sun ce mutanen biyu tsofaffin masoya ne, inda a dalilin kama Buhari da aka yi a kasar Saudiyya na tsawon shekara hudu ya raba masoyan biyu har Maryam ta yi aure kimanin shekara guda da ta wuce.
A tattaunawarsa da manema labarai, Buhari ya nuna nadamarsa game da abin da ya aikata, inda ya ce sharrin Shaidan ne.
Amma ita Maryam ta ce ita a gaskiya ta fi son tsohon saurayinta, don haka a cewarta ba za ta koma gidan mijinta Mohamamd Sani ba.
Mataimakin Kwamandan Hisba na karamar Hukumar Dala, Abubakar Mati Salihu ya ce sun samu nasarar kama wanda ake zargin ne da taimakon ’yan unguwar, wadanda suka sanar wa Hisba inda suka yi zargin matar tana da aure ba matar banza ba ce.
“Lokacin da mutanen unguwar suka sanar mana cewa suna zargin wani ya kawo wata matar aure ya ajiye a gidan, sai muka kama su, muka shiga bincike inda muka gano gaskiyar lamarin,” inji shi.
Abubakar Mati Salihu ya ce, “Yanzu haka muna shirye-shiryen gurfanar da wanda ake zargi gaban kotu domin warware matsalar, musamman ganin yadda matar ta dage cewa ba za ta koma gidan mijinta ba. Kuma muna son kotu ta zartar wa mutumin hukunci game da laifin da ya aikata na boye matar aure.”

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here