Shugaba Muhammadu Buhari Ya Ce Za A Hukunta Wadanda Suka Yi Son Zuciya A Kasafin Kudi

0
1368

Rabo Haladu Daga Kaduna
SHUGABA Muhammadu Buhari, ya sha alawashin daukar tsattsauran matakin ladabtarwa kan duk masu hannu a sassauya alkaluman kasafin kudin shekarar 2016.
Muhammadu Buhari ya yi wannan furuci ne a lokacin da ya gana da \’yan Najeriya mazauna kasar Saudiyya ranar Talata, inda ya yi Allah- wadai da sauye-sauyen da aka yi wa kasafin
kudin.
Shugaban ya kara da cewa sauye-sauyen da aka yi ta bayan fage su ne suka sa kasafin kudin ya bambanta da wanda ya gabatar wa majalisar dokokin
\’\’Wadanda suka tafka wannan danyen aikin ba za su sha ba, sai an hukunta su. Na yi gwamna na mulkin soji, na kuma rike mukamin ministan albarkatun mai da ma shugaban kasa a karkashin mulkin soji, sannan kuma na shugabanci asusun rarar kudin man Fetur; amma ban taba jin wannan kalmar ta \’Budget Padding ba,\’\’ In ji shi.
Shugaba Muhammadu Buhari ya kuma jaddada aniyarsa ta yaki da cin hanci da rashawa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here