Bashir Gatari Ne Ya Lashe Zaben Mazabar Lere Na Kujerar Majalisar Dokoki

  0
  1697

  Isah Ahmed, Daga Jos.

  BASHIR Gatari Idris na jam\’iyyar APC ne ya lashe zaben cike gurbi da aka gudanar a ranar Asabar din da ta gabata a Mazabar Lere ta yamma da ke karamar hukumar Lere a Jihar Kaduna.
  Da yake bayyana sakamakon zaben a garin Lere  babban jami\’in hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa [INEC] Rabi\’u Abdulsalam Magaji ya bayyana cewa \’yan takara hudu ne suka shiga wannan zaben cike gurbi da aka gudanar.
  Ya ce \’yan \’ takarar  su ne Jamilu Yakubu Sulaiman na jam\’iyyar ACPN, wanda  ya sami kuru\’u 61 da  Bashir Gatari Idris na jam\’iyyar APC, wanda  ya sami kuru\’u 17,672 da  Ahmed Mu\’azu Lere na jam\’iyyar PDM wanda  ya sami kuru\’u 328 da kuma  Dokta Mato Dogara na jam\’iyyar PDP, wanda  ya sami kuru\’u 10, 779.
  Ya ce wannan sakamako  ya nuna cewa, Bashir Gatari Idris na jam\’iyyar APC  ne ya lashe wannan zabe da kuru\’u 17,672.
  Da yake zantawa da \’yan jarida bayan bayyana sakamakon zaben Bashir Gatari Idris ya bayyana cewa  babu abin da zai ce wa al\’ummar mazabar Lere ta yamma kan wannan zabe da suka yi masa, sai dai ya yi masu godiya da nuna farin ciki.
  Ya ce a lokacin yakin neman zabe ya zagaya  dukkan lungunan wannan mazaba kuma na ga irin matsalolin da suke damun al\’ummar wannan mazaba. Don haka zan yi iyakar kokarina wajen ganin warware wadannan matsaloli da suke addabar  al\’ummar wannan mazaba.
  Ya yi kira ga al\’ummar wannan mazaba kan su ci gaba da yi masa addu\’a tare da ba shi shawarwari. Ya ce kofarsa a bude take don amsar dukkan shawarwarin da za a ba shi.
  To, amma a zantawarsa da \’yan jarida wakilin jam\’iyyar PDP a wajen tara sakamakon zaben, Alhaji Jumare Tanimu Magaji ya bayyana cewa ba su gamsu da yadda aka gudanar da wannan zabe ba. Don haka za su sake tafiya kotu don su kalubalanci wannan zabe.

   

  LEAVE A REPLY

  Please enter your comment!
  Please enter your name here