Gyaran Kundin Tsarin mulki Zai Taimaka Wa Buhari- Dadari

    0
    2383

    Isah Ahmed Daga Jos

    WANI  malami a sashin binciken aikin gona na Jami\’ar Ahmadu Bello da ke Zariya kuma mai shirhi kan al\’amuran yau da kullum Farfesa Salihu
    Adamu Dadari ya yi kira ga \’yan majalisun Nijeriya da sauran al\’ummar kasa kan a  gaggauta canza kundin tsarin mulkin Nijeriya, domin a
    taimaka wa Shugaban kasa Muhammad Buhari kan yaki da cin hanci da rashawa da yake a kasar nan.

    Farfesa Salihu Adamu Dadari ya yi wannan kiran ne a lokacin da yake zantawa da wakilinmu.

    Ya ce yin hakan ne kadai zai taimakawa gwamnatin Buhari kan wannan kokari da take yi, na yaki da cin hanci a kasar nan.

    Ya ce  alkalai da lauyoyin  Nijeriya idan ka taba su sai su ce tsarin mulkin Nijeriya ne ya ce su yi irin shari\’ar da suke yi a kasar nan a
    halin yanzu.

    Ya ce a lokacin da aka yi wannan kundin tsarin mulki ba a samun masu satar kudaden gwamnati da yawa irin wadanda aka samu a zamanin
    gwamnatocin da suka gabata, don haka babu dokokin da aka tanada don hukumta masu irin wadannan laifuffuka.

    \’\’A yau an wayi gari sai mutum daya ya saci kudi naira miliyan dubu. Kuma idan ka kai wannan mutum kotu, za a ce babu  hukumcin da aka
    tanadar masa a cikin kudin tsarin mulkin Nijeriya. Domin a lokacin da aka yi wannan kundin tsarin mulkin Nijeriya ba a satar irin wadannan
    kudade haka. Don haka dole ne a gyara kundin tsarin mulkin Nijeriya ta yadda za a samar da dokokin da za a rika  hukumta irin waxannan
    varayi. Don haka ya zama wajibi a gaggauta mu hada kai da  \’yan majalisunmu da kowa da kowa a kasar nan,  a samu a  canza kundin
    tsarin mulkin kasar nan, domin gwamnatin Buhari taji dadin tunkarar wannan bala\’i na cin hanci  da ya dabaibaiye Nijeriya\’\’.

    Farfesa Dadari ya yabawa gwamnatin Buhari kan matakan bunkasa harkokin noma da ta dauka. Ya ce babu shakka matakan da wannan gwamnati ta
    dauka na bunkasa harkokin noma, matakai ne masu kyau. Domin  a cikin matakan  akwai maganar farfado da noman  auduga  a Nijeriya, ta yadda
    za a samu a farfado da masakunmu. Wadanda a kalla zasu samarwa da \’yan Nijeriya ayyukan yi, kamar  mutum miliyan 50.

    Har\’ila yau ya ce gwamnati ta ce zata inganta noman shinkafa a kasar nan, domin bai kamata a rika kawo shinkafa daga kasashen waje ba,
    wadda bata kai wadda muke nomawa inganci ba.

    Ya ce manyan kasashen duniya irin su Amurka da Burtaniya da Faransa da Jamus da Caina da Kanada dukkansu ba su yi wani tasiri ba, sai da
    suka rungumi aikin noma.

    Don haka ya yi kira ga al\’ummar Nijeriya kan su ci gaba da yi wa wannan gwamnati addu\’a tare da bata goyan baya domin ta sami nasarar
    kudurorin da ta sanya a gaba.

    LEAVE A REPLY

    Please enter your comment!
    Please enter your name here