IMRANA ABDULLAHI DAGA Kaduna
A kalla Kashi 99.8 na al\’ummar jahar kaduna na cikin akubar wahalar tsadar Ruwan sha a jahar kaduna.
Wannan yanayin da jama a suka tsinci Kansu a ciki musamman ma idan aka yi maganar talakawan kasa da suka dogara da shan Ruwan Leda a matsyin babu wata damar shan Ruwa mai tsafta sai shi.
Sakamakon wannan matsalar da Talakawan Jahar Kaduna suka Shiga a kan Ruwan da za su sha, yasa wakilinmu zuwa ainihin kamfanonin da suke sayar da Ledar da ake buga Ruwan sha da akafi SANI da \”pure water\” wato Ruwan Sha na Leda.
Wakilinmu ya zanta da ainihin ma\’aikatan da Duke sayowa tare da buga Ledar da kuma sayar wa masu sana\’ar yin Ruwan Leda kafin su sayar wa jama\’a musamman masu yin Ruwan shan da Talakawa ke sha, a matsayin abin dogara.
Kamar yadda masu wannan sana\’ar buga Ledar suka shaidawa wakilinmu cewa \”a da can kwanan baya muna sayo Ledar da Mike bugawa jama\’a duk kilogiram daya a matsayin Naira 480 sai mu kuma mu sayar Naira 5020 ko 5030 ga kowane mai gidan Ruwa amma a yanzu sai lamarin ya canza inda Mike sayo duk kilogiram na Leda daga hannun mutanen kasar Indiya da suke kasuwanci a Najeriya muna sayewa me a kan Naira 950 sai mu yi mata aikin Rubuta sunan kamfanoni da Fenti a jikin Ledar mu sayar Naira 1000 ko da dan wani abu ga masu yin Ruwan Ledar\”.
Kuma wakilinmu yaji ta bakin wadannan ma\’aikatan buga Leda tare da sayarwa masu gidajen Ruwan Leda India suka shida masa cewa a duk Leda Kilogiram days ana bugs Ruwan Leda jaka 25 da duk guda ya kuma su suna sayar da kwarkwaro daya yana da nauyin Kilogiram 16 saboda haka idan aka yi lissafin yadda suke sayarwa za a Tara kudin Kilogiram Naira dubu daya da naira Hamsin sau 16 kamar yadda ake sayarwa.
Wannan matsalar tasa daukacin jama\’a musamman Talakawa suka samu Kansu a cikin wahalar samun Ruwan da za su jika makoshi sakamakon rashin tsaftataccen Ruwan da za su sha.
Wasu masu gidajen Ruwan sha na Leda da aka fi SANI da \”pure water\” da acan baya suke sayar da Ruwan a kan kudi Naira Hamsin ko Wanda yake da kyau a kan Naira Sittin ga masu shaguna da sauran masu sayar da Ruwa suke sayar wa jama\’a duk kwaya daya na Ruwa a matsayin naira biyar ga duk mai son saye.
Amma a halin yanzu kudin ya koma Naira Goma a kowane kwayar Ledar Ruwan sha, a wasu wuraren kuma ya koma Naira 20 ga kowace kwayar Ledar Ruwan Sha.

Kamar yadda wakilinmu da ya halarci wadansu unguwanni a cikin garin kaduna da kewaye jama\’a sun bayyana cewa suna sayen Ledar Ruwan ne a kan Naira 150 a wani wurin kuma duk Leda a kan Naira 180,Wanda a baya ake sayarwa a kan Naira 50 ko 60.
Wakilinmu yaji ta bakin masu buga Ledar na cewa idan mutum ya sayi Leda mai nauyin kilogiram 16 zai buga Ruwa jaka 400 Wanda idan an sayar da shi Naira 100 a kowace jaka za su iya samun ribar sama da dubu ashirin, amma kuma ana gallazawa Talakawa da suka dogara da shan Ruwan Leda.
Sai dai kuma ana ta batun cewa ko hukumar kwastan ta kara wa kamfanonin mutanen da suke shigowa da Ledar daga kasashen wake kudin harajin kaya.
A bisa lissafin da muka yi ya bayyana karara cewa ga duk wanda ya sayi Ledar yin Ruwan sha mai nauyin kilogiram 16 da kudinta zai kama sama da dubu 16 kamar yadda masu kamfanin sayar da ita suka yi mana bayani,za\’a iya samun jakar Ruwan sha da Ruwa kwara 20 ke ciki za a samu jaka 400 da idan aka sayar da kowace Jaka a kan kudi Naira 100 za\’a samu Naira dubu 40,000 ga kowane kilogiran 16,wanda kamar yadda lissafin ya kama za\’a samu riba ta fito ta naira 23200.

Jama\’a da dama na yin kira ga gwamnatin jahar kaduna da kuma duk kan sauran hukumomi cewa su SA idanu ga irin yadda karamar hukuma ke karbar haraji daga masu gidajen buga Ruwan Leda ko kamfanonin yin Ruwan kwalba domin jama\’a su samu sauki.
Duk kokarin jin ta bakin masu kamfanonin yin Ruwan lamarin ya ci tura saboda duk gidan Ruwan da ka tunkara masu kamfanin basa son yin magana game da lamarin sai dai kawai su ce kaya ne suka yi tsada.
Sai dai wannan lamari ya jefa Talakawa cikin wata sabuwar akuba ganin cewa daman talakawan ne masu dan karfi daga cikinsu ke samun fitar da dan abin cikin aljihunsu su sayi Ruwan Naira biyar da nufin ganin sun sha Ruwa mai tsafta domin inganta lafiyarsu daga cututtukan zamani ta yadda za\’a gujewa kudin biyan asibiti da na magunguna.