Ba A Bukatar Jahohi 36 A Najeriya -Shehu Sani

0
1113

SANATA mai wakiltar kaduna ta tsakiya kwamared Shehu Sani ya fito fili ya bayyana cewa a tarayyar Najeriya babu bukatar jahohi 36 da ake da su a halin yanzu.

Sanata Shehu Sani, ya bayyana hakan ne a lokacin da yake ganawa da kungiyar masu wallafa jaridu a kafar Intanet na Arewacin Najeriya da suke da ofishi a kaduna.

Shehu ya ci gaba da cewa idan aka yi la akari da irin yadda a halin yanzu al\’amarin mai ya yi kasa a duk fadin duniya za a tabbatar da cewa lallai babu bukatar jahohi 36 kamar yadda ake da su a halin yanzu.

Da irin wannan mataki na rage jahohi su koma 6 batun gwamnoni su da wasu mukarrabansu su rika zuwa Abuja domin rabon kudi duk wata wata an huta da shi baki daya.

\”Abin da ya dace shi ne jihohi masu shiyya kamar haka a yankin Arewa maso Yamma hedikwata Kaduna,Arewa ta tsakiya Filato sai Arewa maso Gabas a Barno da kuma Fatakwal,Enugu da Legasa tare da Abuja a matsayin birnin tarayyar kasa\”.

Ya tabbatar da cewa idan aka yi haka za a ga gagarumin ci gaba a kasa baki daya saboda Iowa zai samu walwala hankalin jama a ya dawo jikinsu dan kankanin lokaci.

A batun masu kokarin cin bashi kuwa Sanata Sani cewa ya yi duk wani gwamnan da zai ci bashi sai sun tace shi sosai suga ko ya cancanci gwamnati ta bashi dama ya ciwo bashi daga wata kasa domin lokacin yin wakaci ka tashi da dukiyar jama a ya wuce,bin ka ida da doka shi ne kawai mafita.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here