An Ba Mata 5,740 Tallafin Awaki A Jigawa

0
1152

Daga Usman Nasidi

Mata 5,740 ne gwamnatin Jigawa ta bai wa tallafin awaki 17,220 a kokarinta na taimaka wa matan da mazajensu suka rasu domin su samu damar daukar nauyin marayun da aka bar musu.

Mai bai wa Gwamnan Jihar Jigawa shawara a kan harkokin tallafa wa matasa Malam Muhammad Sheikh Mujaddadi, inda ya ce an bai wa matasa 125 kadada dubu uku domin yin noman rining a jihar kuma gwamnati ta ba su gudunmawar da suke bukata.

Malam Muhammad Mujaddadu ya kara da cewa gwamnatin jihar ta samo wani kamfani mai suna WASCOT a matsayin wanda zai sayi
kayayyakin daga wajensu bayan sun noma.

Ya ce shirin noman za a gudanar da shi ne a mafi yawan kananan hukumomin jihar da suke yin noman rani.

Acewarsa Hukumar Bunkasa kasashe ta kasar Ingila (DFID) ta dauki mata 450.daga karamar Hukumar Miga da Malam Madori da Ringim domin koya musu sana’ar hannu don su rika dogaro da kansu.

Mashawaracin Gwamnan ya ce an bai wa matasa 3,375 horo a kan harkar aikin maganin dabobi da aka dauko sudaga wadancan kananan hukumomi uku da aka amba ta a baya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here